Kel Ahaggar

Kel Ahaggar

Kel Ahaggar (Berber: ⴾⵍ ⵂⴴⵔ) (trans: "Mutanen Ahaggar") ƙungiyar Abzinawa ce da ke zaune a tsaunin Hoggar (Dutsen Ahaggar) a cikin Aljeriya. An yi imanin cewa babban magidancin Abzinawa Tin Hinan ne ya kafa kungiyar, wanda kabarinsa yake a Abalessa. Kafuwarta a hukumance tana da kwanan wata kusan dubu ɗaya da ɗari bakwai da hamsin 1750. An daina aiki da shi tun shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da bakwai 1977, lokacin da gwamnatin Aljeriya ta kawo karshen ta.

Harshen ƙungiyar shine Tahaggart, yaren Tamahaq.


© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search